
Rundunar yan sandan jihar katsina ta ce jami’anta sun ceto wasu fasinjoji 5 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Faskari ta jihar.
Abubakar Aliyu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya fadawa manema labarai ranar Talata a Katsina cewa anyi garkuwa da fasinjojin ne a ranar 19 ga watan Mayu a kauyen Unguwar -Basau dake kan titin Funtua zuwa Gusau.
” A ranar 19 ga watan Mayu ofishin yan sanda na shiya dake Fasakari ya samu kiran kai daukin gaggawa da misalin karfe 09:37 na dare dake cewa yan bindiga sun kai farmaki kan wasu fasinjoji dake cikin wasu motoci biyu a Unguwar Basau dake kan titin Funtua zuwa Gusau,” ya ce
“Motocin da aka kaiwa hari sun hada da Hummer bas mai namba T0510 KN da kuma wata farar babbar mota kirar Mendez mai namba LFA 508 YR.”
Samun rahoton ke da wuya jami’an yan sanda suka garzaya wurin a cikin motar sulke ta sintiri inda suka fatattaki yan bindiga kuma suka ceto mutanen da suka hada da direbobi biyu da kuma fasinjojin.