Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri, wanda ya dauki tsawon shekaru goma yana karbar dubban mutane da suka rasa matsuguni sakamakon rikicin Boko Haram. A cewar gwamnan, sansanin yana dauke da fiye da mutane 11,000 kafin rufewa.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa matsalolin da ke ci gaba da faruwa a cikin sansanin sun hada da karuwanci, tada hankula, cin zarafin yara da kuma aikata wasu laifuka na daban, lamarin da ya sa gwamnati ta yanke shawarar rufe sansanin.
“Mun ga yadda harkokin da ba su dace ba ke karuwa a cikin sansanin. Akwai karuwanci, miyagun kungiyoyi, cin zarafin yara da sauran laifuka. Wannan yasa muka yanke hukuncin rufe sansanin Muna,” in ji Gwamna Zulum.
Ya kara da cewa babu yadda za a gama da Boko Haram idan har mutane ba su koma garuruwansu ba. A cewarsa, dole ne a samar da hanyoyin dogaro da kai ga wadanda rikicin ya raba da gidajensu domin zaman lafiya da dorewa.
Tun a shekara ta 2021, Zulum ya sha alwashin rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira 12 da ke cikin birnin Maiduguri. Ya rufe su duka sai sansanoni biyu da ba na gwamnati ba, ciki har da na Muna wanda yanzu aka karshe da shi.
A cikin shekara ta 2024, gwamnatin jihar ta riga ta mayar da kusan kashi 75 cikin 100 na mazauna sansanin Muna zuwa garuruwansu na asali. Yanzu, saura kashi 25 cikin 100 daga cikin su za su koma gida a cikin kwanaki masu zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa, domin saukaka musu rayuwa, kowanne gida daga cikin gidaje 6,000 da ke sansanin zai samu kayan abinci, kayan gini da kuma kulawar lafiya. Haka kuma, dukkan shugaban gida – ko mace ko namiji – za su samu Naira 100,000, tare da karin Naira 50,000 ga matan gida.
Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnatin Zulum na dawo da martabar mutanen da rikici ya shafa tare da rage dogaro da taimakon gaggawa.
Gwamna Zulum Ya Rufe Sansanin Muna, Ya Bukaci ‘Yan Gudun Hijira Su Koma Gidajensu
