
Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kaddamar da bincike kan mutuwar wasu yara 5 a cikin wata mata da aka ajiye ba amfani da ita.
Lamarin ya faru ne a Agyaragu karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Rahman Nansel mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an gano gawar yaran ne a cikin wata tsohuwar mota da ke ajiye a harabar gidan wani mai suna Abu Agyeme.
Yaran da suka mutu sun hada da Kamsi Onah(namiji mai shekaru 8) Soner Onah(namiji mai shekaru 6) Eunice Udouchi ( mace mai shekaru 10) Mmsoma Nnaji (mace mai shekaru 10) da kuma Chioma Nnaji (mace mai shekaru 8).
A ranar 04 ga watan Mayu ne wata mai suna Ozimna Ogbor mazauniyar Agyaragu ta shigar da korafi a ofishin yan sanda na Agyaragu cewar an gano wasu yara basa motsi a cikin motar dake ajiye.
Samun rahoton faruwar lamarin ke da wuya kwamishinan yan sandan Shettima Jauro Mohammed ya umarci DPO din yan sandan yankin da jami’ansa da su gaggauta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Nansel jami’an sun dauki yaran ya zuwa asibitin dake kusa inda aka tabbatar da mutuwarsu.