Ba Wanda Zai Iya Zama Shugaban Ƙasa Ba Tare Da Goyon Bayan Arewa Ba, A Cewar Baba-Ahmed

Tsohon mai magana da yawun Kungiyar Tsofaffin Shugabannin Arewa kuma tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara a kan harkokin siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu ɗan siyasan da zai iya zama shugaban ƙasar Najeriya ba tare da goyon bayan yankin Arewa ba.

Baba-Ahmed, wanda kwanan nan ya ajiye aikinsa a matsayin mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara, ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa da ke yawo a kafafen sada zumunta tare da Farfesa Usman Yusuf, tsohon Sakataren Hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS).

Ya ce: “Babu ɗan siyasar da zai iya zama shugaban ƙasa ba tare da goyon bayan Arewa ba.”

Ya kuma bayyana cewa Arewa za ta bayyana matsayinta na siyasa gabanin zaɓen 2027 cikin watanni masu zuwa.

“A cikin watanni shida masu zuwa za ku ji abin da Arewa za ta yi. Ba za mu ɓoye ba,” in ji shi.

Dr. Baba-Ahmed ya jaddada cewa Arewa ta fuskanci matsanancin ƙunci, musamman a lokacin da rikicin Boko Haram ya fi kamari, inda rayuka da dukiyoyi suka salwanta a fannoni daban-daban.

“Mun sha wahala. Mun san mene ne ƙunci. Muna buƙatar gwamnati da za ta fahimci damuwarmu kuma ta magance ta,” in ji shi.

Ya yi gargadi ga duk wani yunkurin ware Arewa daga tafiyar siyasa, yana mai cewa hakurin yankin na ƙarewa.

“Idan suna shirin murɗe zaɓe, su yi hattara. Ba zai yi wa ƙasar nan kyau ba,” a cewarsa.

Ya kara da cewa al’ummar Arewa yanzu sun fi wayewa a siyasa fiye da da, kuma ba za su sake yarda su yi ruɗu da alkawuran ƙarya ko siyasar raba kan jama’a ba.

More from this stream

Recomended