Shehu Sani ya shawarci Tinubu da ya guji nuna son kai wajen nada mukamai

Tsohon sanata mai wakiltar yankin Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya guji nuna son kai da fifita ƙabilarsa wajen naɗa manyan mukamai a gwamnatin tarayya.

Sanata Shehu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Channels Television a cikin shirin “Politics Today” a ranar Alhamis, inda ya caccaki yadda yawancin shugabannin Afirka ke cike manyan kujeru da ‘yan ƙabilarsu da zarar sun hau mulki.

“Ina roƙon shugaban ƙasa Asiwaju ya yi hattara kada ya bi wannan hanyar, domin abu ne da ya zama ruwan dare a siyasar Afirka: duk wanda ya hau mulki sai ya rika ɗora ‘yan ƙabilarsa a manyan wurare. Wannan yana faruwa a ko’ina,” in ji Shehu Sani.

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa shugabanni su daina kallon mulki a matsayin wata ganima da za su raba wa ‘yan uwansu, su ɗauke shi a matsayin dama ta yi wa al’umma hidima ba na nuna wariya ba.

Rahotanni daga sun nuna cewa shugaba Tinubu ya fuskanci suka daga ‘yan adawa da ma wasu manyan ‘yan siyasa na jam’iyyarsa ta APC, dangane da abin da ake kira da nuna son kai wajen naɗin mukamai – musamman yadda aka fi bai wa ‘yan yankin Yarbawa manyan kujeru a gwamnatinsa.

A baya, Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattijai daga Borno ta Kudu, ya zargi gwamnatin Tinubu da karya tsarin wakilcin ƙasa (Federal Character), yana mai cewa hakan na iya haifar da illa matuƙa idan ba a gyara ba.

Sai dai mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya mayar wa Sanata Ndume da martani, yana zarginsa da ruɗani da rashin gaskiya.

Shehu Sani ya kuma yi kakkausar suka ga ‘yan adawar da ke cika da surutu a yanzu amma suka yi shiru lokacin da ‘yan ƙabilarsu ke aikata irin wannan abu.

More from this stream

Recomended