Wani dan majalisar wakilai daga Bassa/Jos ta Arewa, Daniel Asama, ya bayyana cewa jami’an tsaro na da masaniya game da wadanda ke da hannu a hare-haren kisa da ake ta fama da su a Jihar Filato, inda ya bayyana lamarin a matsayin kisan kare dangi.
Asama ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na Channels Television a safiyar Alhamis, inda ya ce fiye da mutane 100 ne aka kashe cikin makonni biyu da suka gabata a jihar.
“Jami’an tsaro sun san inda hare-haren ke tasowa. Sun san hanyoyin da ake bi. Mutanen yankin za su iya nuna musu hanyoyin da masu hari ke bi idan aka basu dama,” in ji shi.
Ya kara da cewa bai yadda da cewa jami’an tsaro ba su san inda masu kai hare-haren suke ba. “Idan har jami’an tsaro suka hada kai da al’ummar yankin, za su samu cikakken bayani da suke bukata.”
Dan majalisar ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren ke kara rura wutar tashin hankali, tare da korar jama’a daga gidajensu, yana mai danganta lamarin da yunkurin kwace filaye da karfin tsiya.
Jawaban Asama na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara matsa lamba ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen matsalolin tsaro a jihar Filato da sauran sassan kasar nan.
’Yan Sanda Sun San Masu Kashe Jama’a a Jihar Filato — Dan Majalisa
