
Matatar mai ta Dangote ta sake rage farashin kuɗin litar man fetur da take sayarwa dillalan mai ya zuwa ₦835 kan kowace lita.
A cewar wasu majiyoyi dake matatar man ta rage farashin kuɗin mai da take sayarwa da dillalan mai ya zuwa ₦835 kwanaki 6 bayan da matatar ta rage kudin ya zuwa ₦865 kowace lita.
Wata majiya dake matatar ta fadawa jaridar The Cable tabbas an rage farashin kuɗin litar man.
Rage farashin kuɗin litar man fetur da matatar tayi na zuwa ne biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya tayi a ranar 9 ga watan Afrilu cewa za a cigaba da sayarwa matatar ɗanyen man fetur akan kuɗin naira.