An hana kiwon dabbobi da daddare a jihar Filato

Caleb Mutfwang gwamnan jihar Filato ya sanar da hana kiwon dabbobi da daddare tare da taƙaita yin amfani da baburan hawa a faɗin jihar biyo bayan yawan hare-haren da ake kaiwa a jihar.

Aƙalla mutane 50 aka bada rahoton sun mutu bayan da ƴan bindiga suka kai farmaki ƙauyen. Kimakpa dake gundumar Miangu a karamar hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.

Da yake magana a lokacin wani jawabi da ya yiwa al’ummar kuma aka watsa ta kafafen yaɗa labarai na jihar a ranar Laraba gwamnan ya kuma hana jigilar shanu a mota bayan ƙarfe 07:00 na dare.

Mutfwang ya ce umarnin ya fara aiki nan take kuma takaita zirga-zirga da babur za ta fara aiki daga ƙarfe 07:00 na dare ya zuwa 06:00 na safe har ya zuwa wani lokaci anan gaba.

Ya bayyana kisan a matsayin wani tsararren abu da aka shirya domin raba mazauna jihar da muhallinsu da kuma tauye musu yancin su na zama lafiya a ƙasar su.

More from this stream

Recomended