Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki a garuruwan Banga da Larh da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa, inda suka kashe mutane bakwai tare da lalata dukiya da dama.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya auku ne da daren Talata, 15 ga Afrilu, 2025, inda ‘yan ta’addan suka shigo garuruwan cikin dare suka bar su da raunuka da asara mai yawa.
A cewar wani shaidar gani da ido, mutum hudu ne suka rasa rayukansu a Banga, ciki har da wani dan sa-kai da bam ya kashe, wasu maza biyu da aka harbe kai tsaye, da wata mata da ta mutu yayin da take kokarin tserewa.
A Larh kuwa, mutane biyu aka kashe, sai kuma karin mutum daya da wata majiya mai karfi ta tabbatar da mutuwarsa, wanda hakan ke nufin cewa adadin wadanda suka mutu ya kai bakwai.
Daya daga cikin kadarorin da aka lalata akwai motar ‘yan sanda daga Garaha da ke ajiye a Banga, wadda bam na Boko Haram ya tarwatsa. Sai dai babu wanda ya rasa ransa a cikin motar, domin dukkan ma’aikatan sun bar motar kafin fashewar ta faru.
Haka zalika, wani karamin yaro bai dawo gida ba bayan harin, inda wani dan unguwa ya bayyana cewa, “Ana kiran wayarsa amma ba ya dauka.”
Shugaban karamar hukumar Hong, Usman Wa’aganda, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da aka yi da shi da rana a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka mutu.
Wannan hari na zuwa ne mako guda bayan sarkin gargajiya na yankin Hong ya sha alwashin cewa ‘yan Boko Haram ba za su sake samun damar tada zaune tsaye a yankin ba.