Ƴan bindiga sun kashe Sinawa biyu da ɗan sanda a Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kashe ƙwararrun ma’aikata biyu ’yan ƙasar Sin da jami’in tsaronsu a ƙaramar hukumar Isuikwuato da ke jihar Abia.

Kakakin rundunar, DSP Maureen Chinaka, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Ta ce harin ya faru ne a garin Uturu yayin da tawagar ma’aikatan Sinawa ke kan hanyarsu zuwa wurin aiki da ke Agukwu-Amaya, a Ndundu, a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.

DSP Chinaka ta ce maharan sun kashe manajan kamfanin, Mr. Quan, da abokin aikinsa, Mr. Cai, tare da ɗaya daga cikin jami’an sintirin, Inspector Audu Saidu, inda suka kwace bindigarsa bayan sun harbe shi.

Sai dai, ta ce jiki kadan bayan sun samu bayanin kai harin, jami’an rundunar ’yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da aikin ceto.

A sakamakon haka, sun samu nasarar ceto wasu ’yan kasar Sin guda uku ba tare da rauni ba, yayin da ɗaya daga cikinsu ya samu rauni.

Bugu da ƙari, jami’in ’yan sanda mai suna Inspector Uba Ahmed ya tsira amma da harbin ƙafa. Yanzu haka yana karɓar magani tare da sauran waɗanda suka jikkata a asibitin FMC Abakaliki.

More from this stream

Recomended