An kai wani sabon hari kan sojoji daga Bataliya ta 312 da ke Barikin Kalapanzi a jihar Kaduna, inda aka kashe soja guda daya yayin da wani ya jikkata.
Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ‘yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Ya ce majiyoyin tsaro sun sanar da shi cewa wasu mahara uku dauke da makamai sun harbi sojojin, inda suka kashe daya mai suna Kofur James (sai dai ba a san sunan mahaifinsa ba) sannan suka jikkata Farfesan Ibrahim Bazalla.
Bayan harin, ‘yan bindigar sun kwace bindigogi biyu kirar AK-47 daga hannun sojojin kafin su tsere.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Sojoji na 44, inda aka tabbatar da mutuwar Kofur James, yayin da ake ci gaba da jinya ga Farfesan Bazalla.
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wa Sojoji a Kaduna Inda Suka Hallaka Guda Daya
