Ƴan sanda sun gano motocin sata 19 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta  sanar da cewa ta gano motocin sata 19 da aka sace a birnin a tsakanin watannin Fabrairu da Maris na shekarar 2025.

Kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja,Olatunji Rilwan Disu ne ya bayyana haka lokacin da yake nunawa ƴan jaridu motocin da aka gano a hedkwatar rundunar dake Abuja a ranar Talata.

Ya ce wasu daga cikin motocin an sace su ne a Abuja amma kuma an samu nasarar gano su a jihohin Filato, Kaduna da kuma Neja ta hanyar ofisoshin yan sandan daban-daban.

Ya ce ofishin yan sandan na Mpape sun samu nasarar gano uku daga cikin motocin, na Maitama sun gano daya da sauran ofisoshin ƴan sanda daban-daban dake birnin.

Kwace da kuma satar abun hawa abu ne dake neman zama ruwan dare a birnin na Abuja duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi wajen daƙile ayyukan ɓata garin dake aikata laifukan.

More from this stream

Recomended