NMDPRA Ta Ba Da Lasisin Buɗe Sabbin Matatun Mai a Najeriya

Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Ƙasa (NMDPRA) ta ba da lasisi ga wasu kamfanoni uku don buɗe sabbin matatun mai a jihohin Abia, Delta, da Edo.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa Matatar Eghudu, da za a gina a Edo, za ta iya tace ganga 100,000 na mai a kullum.

Haka kuma, a jihar Delta za a gina Matatar MB da za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum, yayin da Matatar HIS da ke jihar Abia za ta tace ganga 10,000 a kullum.

Jimilla, idan an kammala su, sabbin matatun za su riƙa tace ganga 140,000 na mai a kowace rana.

More from this stream

Recomended