Kwamshina ya mutu a jihar Cross River

Robert Ewa,  kwamshinan yawon buɗe masa ido da al’adu na jihar Cross River ya mutu.

Nsa Gill mai magana da yawun gwamnan jihar shi ne ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Gill ya ce marigayin ya mutu ne a wani asibiti dake jihar.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce kwamishinan ya halarci taron majalisar zartarwar jihar na ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa Ewa ya tofa albarkacin bakinsa a lokacin taron kafin daga bisani ya nemi a sahale masa ya tafi gabanin kammala taron.

“Gwamna ya kaɗu sosai da samun labarin mutuwarsa amma za a fitar da sanarwa a hukumance kan mutuwarsa,” a cewar Nsa.

More from this stream

Recomended