Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS da ta gaggauta sako, Bello Bodejo shugaban kungiyar Miyettti Allah Kautal Hore.
Alƙalin kotun, Mohammed Zubairu shi ne ya bayar da umarnin a ranar Talata biyo bayan buƙatar gaggawa da Reuben Alabo lauyan Bodejo ya gabatar a gaban kotun.
A ranar 9 ga watan Disamba ne iyalan Bodejo suka bayyana cewa an kama Bodejo sakamakon wani rikici da ya faru tsakanin wasu makiyaya da wani tsohon Janaral na soja.
A cewar iyalan wasu sojoji daga Batalita ta 117 dake Maliya a jihar Nasarawa ne suka kama Bodejo.
A ranar 19 ga watan Disamba Bodejo ya shigar da karar ministan shari’a da kuma shugaban hukumar DSS kan yadda su ke cigaba da tsare shi ba tare da sun gurfanar da shi a gaban kotu.