Yan bindiga sun kashe wani baƙo a cikin Otal a jihar Ogun

Ƴan bindiga sun kashe, Gideon Ebukwe wani baƙo da ya sauka a otal ɗin Ok Winners dake Igbosoro  a garin Shagamu na jihar Ogun.

An ce lamarin ya faru bayan da wasu mutane da ba a gane ko su waye ba suka isa Otal ɗin inda suka ƙulle ma’aikatansa a wani ɗaki kafin su shiga ciki su fara neman Ebukwe.

Omolola Odutola mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce Atobatele Igbosoro shugaban kungiyar cigaban al’ummar yankin shi ne ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin ƴan sanda da ƙarfe 03:30 na ranar Talata.

Odutola ya ce ba a kama mutanen da ake zargi da kisan kan ba kuma tuni aka kai gawar dakin ajiye gawarwaki.

Ya tabbatarwa da al’umma cewa an kaddamar da bincike domin gano yanayin laifin ya ƙara da cewa an kuma tura laifin zuwa hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar dake Abeokuta domin cigaba da bincike.

“A lokacin harin ma’aikatan otal ɗin da Yawancin su mata ne an ƙulle su a wani dakin a yayin da maharan suka wuce kai tsaye dakin bakon,” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended