Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta bayyana a ranar Litinin cewa zarge-zargen wulakanci ga Naira da ake yi wa Hajiya Fauziya Danjuma Goje, ‘yar Sanata Danjuma Goje, ba su da tushe.
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga ana watsa Naira a wurin wani biki a Kano ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2024. Wannan ya sa jama’a suka yi tunanin cewa bikin nata ne, inda suka nemi a hukunta ta tare da sauran wadanda suka halarci wajen saboda wulakanci ga Naira.
A cikin wata sanarwa da Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, hukumar ta tabbatar cewa bidiyon ya nuna tabargazar wulakanci ga naira, amma ba a bikin ‘yar Goje aka yi lamarin ba.
Oyewale ya bayyana cewa bikin ya faru ne a wajen liyafar bikin Hajiya Amina Babagana Zannah, ‘yar Hajiya Hajara Seidu Haruna (wadda aka fi sani da Hafsat Gold Nigeria), wacce ita ce mai kamfanin kayan adon Hafsat Jewellery Enterprise mai rassan a Abuja, Kano, da Dubai.