Hukumar tsaro ta NSCDC da aka fi sani da Civil Defense ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wani direban tankar mai ta NNPCL da aka samu da laifin karkatar da mai har lita 10,000.
Igbalawole Sotiyo kwamandan NSCDC a jihar Osun shi ne ya bayyana haka lokacin da yake nunawa manema labarai direban tare da yaransa biyu a Osogbo babban birnin jihar.
Sotiyo ya ce wanda ake zargin ya ɗauko litar mai 40,000 daga kamfanin Pinnacle dake yankin Eleko a jihar Lagos amma sai kawai ya sauke lita 30,000 a gidan man na NNPCL.
Ya ƙara da cewa an kama shi ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 08:21 na dare bayan da aka tsegunta musu bayanin cewa yana sauke sauran litar man a gidan man Tempola dake Ikirun a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar.
Kwamanda ya ce wanda aka kaman ya amsa laifin karkatar da ragowar man fetur.