Jami’an yan sanda 5 sun mutu a wani hatsarin mota a Kano

Jami’an ƴan sandan biyar ne suka mutu a yayin da wasu 11 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Zaria zuwa Kano.

Hatsarin ya faru ne lokacin da motar da jami’an ƴan sandan suke ciki ta ci karo da wata babbar mota.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru da safiyar ranar Talata a garin Karfi dake ƙaramar hukumar Kura ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faɗawa jaridar Punch cewa hatsarin ya faru ne lokacin da jami’an suke kan hanyarsu ta dawowa daga wurin wani aiki da suka je.

Ya ƙara da cewa jami’an da suka jikkata na can na samun kulawa a wani asibiti dake birnin Kano.

More from this stream

Recomended