Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a yankin Ibeju-Lekki da ke jihar a ranar Juma’a.
Wadanda ake zargin sun hada da Victor Okoman mai shekaru 24, Saheed Balogun mai shekaru 38 da kuma David Kaimon mai shekaru 27.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, babban Sufeton ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X (Twitter a baya), da yammacin Juma’a.
“Jami’an sashen Elemoro sun amsa kiran gaggawa a yau, Juma’a, 20 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 0200 na safe kimanin wasu matasa uku da suka yi wa masu wucewa fashi da bindiga, inda suka kama Victor Okoman mai shekaru 24, Saheed Balogun mai shekaru 38 da David Kaimon, mai shekara 27 dauke da wata karamar bindiga mai dauke da kayan alburusai,” in ji Hundeyin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya kara da cewa wadanda ake zargin sun jagoranci ‘yan sanda wajen kwato alburusai guda 26.
Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.