Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar suka samu kiredit biyar zuwa sama a harshen Ingilishi da lissafi.

Shugaban NECO Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar NECO a ranar Alhamis da ta gabata a garin Minna na jihar Neja.

Farfesa Wushishi ya bayyana cewa mutane 1,376,423 da suka kunshi maza 706,950 da mata 669,473 ne suka yi rijistar jarabawar.

Shugaban na NECO ya yi karin haske kan sakamakon: “Yawan wadanda suka zana jarrabawar sun kai 1,367,736, wadanda suka kunshi maza 702,112 da mata 665,624. 

“Yawancin wadanda suka sami maki biyar da sama da haka, ciki har da Ingilishi da Lissafi, sun kai 828,284, wanda ke wakiltar kashi 60.55%.

More from this stream

Recomended