Ƴanbindiga sun kashe mutane a Filato

Wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane biyar a kauyen Mbar da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Sanarwar da Barista Farmasum Fuddang, shugaba, da Amb.  Duwam Bosco, sakataren kungiyar Bokkos Cultural Development Council Vanguard (BCDCV), a Jos, ita ta bayyana hakan.

A cewarsu, “Muna so mu yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyar da ba su ji ba ba su gani ba a yankin Mbar a ranar 15 ga watan Satumba, duk da rahotannin sirri da aka samu a baya na kwararar ‘yan ta’adda a yankin.”

Sanarwar ta bayyana cewa, an far wa matasan, wadanda ba su da makami, a kan hanyarsu ta daga garin Mbar zuwa kauyen Koh a kan wata hanya da ta kewaya kauyen Yelwa Nono da misalin karfe 7 na dare zuwa karfe 7:30 na dare, inda ‘yan ta’addan suka tsere kan babura wadanda tun farko sojoji suka fatattake su daga kewayen wajen.

Jihar Filato dai takan fuskanci irin waɗannan hare-haren.

More from this stream

Recomended