Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.

Mista Ngelale ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

“A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa inda na sanar da ofishina cewa zan tafi hutu don tunkarar al’amuran kiwon lafiya da suka shafi iyalina. 

Wannan na zuwa a daidai lokacin da lamura suka rincaɓe a Najeriya, musamman ta fuskar tattalin arziki.

More from this stream

Recomended