Zaben PDP: Lissafi ya kwacewa wasu ‘yan takara, an daina jin amon muryar su

 

A yanzu haka wakilai da zasu kada kuri’a, mambobi da ragowar masoya da masu goyon bayan jam’iyyar PDP na can garin Fatakwal na jihar Ribas domin zaben dan takarar shugaban kasa daga cikin ‘yan takara 12. 

Sai dai daga rahotanni dake shigowa daga al’amuran siyasa dake gudana a can garin Fatakwal, an daina jin amon muryar wasu ‘yan daga cikin ‘yan takarar da a baya sunansu ke yin amo.

 

Takara ta koma kusan tsakanin mutane uku: tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

 

Wasu rahotanni na nuna cewar dattijai da wasu masu ruwa da tsaki a PDP sun fi son ganin Tambuwal ya samu nasara a zaben. Tuni aka fara yada labaran cewar wasu daga cikin ‘yan takarar sun janye masa kafin daga bisani su fito su musanta hakan.

 

Yayin da ake ta wannan sa-toka-sa-katsi, sunayen wasu manyan ‘yan takara ya bace, ko kadan ba a jin duriyar su.

Daga cikin irin wadannan ‘yan takara akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da takwaransa na jihar Jigawa, Sule Lamido, da tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

Ragowar su ne Datti Baba Ahmed da Stanley Osifo da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.

 

Wata majiya ta bayyana cewar tsohon minista Tanimu Turaki ya janyewa Saraki takarar sa, har ya zuwa wannan lokaci bai fito ya musanta wannan rahoto ba.

Jama’a dai sun yi matukar mamakin yadda kwata-kwata ba a zancen Sule Lamido da Sanata Kwankwaso.

Wani labari da ke yawo a tsakanin ‘yan siyasar Kano na bayyana cewar tun ranar Juma’a aka kwashe daliget din jihar Kano ba tare da sanin Kwankwaso ba.

Shi kuwa Sule Lamido cewa aka yi ya janyewa Tambuwal, kuma har yanzu shi ko wani wakilinsa bai musanta wannan rahoto ba.

Lamarin dusashewar sunan Kwankwaso da Lamido ya bawa mutanen arewa mamaki, musamman ganin gogewa da dadewar su a fagen siyasa.

More from this stream

Recomended