Rahotanni daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 150 tare da sace shanu sama da 1,000 a kauyukan da ke masarautar Gobir ta jihar Sokoto.
Idan ba a manta ba, an yi garkuwa da Sarkin na Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, kuma Hakimin Gatawa a ranar 29 ga watan Yuli tare da dansa da wasu mutane shida a hanyar Sokoto zuwa Sabon Birni.
Wani faifan bidiyo mai daure kai ya nuna Sarkin yana rokon a biya masa kudin fansa kafin rasuwarsa, lamarin da ya kai ga zanga-zanga a yankin da kuma dokar hana fita a Sabon Birni.
Masu aiko da rahotanni sun tattaro cewa ayyukan ‘yan fashin na baya-bayan nan ya sake sanya damuwa kan ayyukan da suke yi a yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, SP Ahmad Rufa’i, ya bayyana cewa ba a samu wani rahoto a hukumance ba amma za su ci gaba da bincike kan lamarin.
Ƴan bindiga sun yi awon-gaba da sama da mutum 150 da shanu 1,000 a Gobir kwanaki kaɗan bayan kashe sarkinsu
Date: