An kama wasu ƴanta’adda da ke da alaƙa da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya. 

Jami’an tsaron Najeriya ne suka kama mutanen a kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar, biyo bayan kisan gilla da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Hakimin gundumar Isa Muhammad Bawa.

Wani faifan bidiyo ya nuna ‘yan ta’addan da aka kama suna tsare a wani dandali, ana yi musu tambayoyi daga jami’an tsaro.

More from this stream

Recomended