10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaUwargidan Tinubu ta yi rabon buhunan shinkafa a Jihar Bauchi

Uwargidan Tinubu ta yi rabon buhunan shinkafa a Jihar Bauchi

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bayar da gudummawar buhunan shinkafa 25kg ga gidaje 2,400 a jihar Bauchi. 

An sanar da hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da AIT ta saka a shafinta na X ranar Talata.

Uwargidan Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, Aisha Bala, ta tabbatar da wannan karimcin na uwargidan shugaban kasar, inda ta kara da cewa ofishinta ya kuma baiwa kowannen wadannan gidaje naira 10,000. 

“A yau, muna ƙara shaida wani muhimmin abu na rabon abinci ga mutane 2,400 ta Renewed Hope Initiative, watau gidauniyar uwargidan shugaban kasar Najeriya, inda kowane daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin zai karbi buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da kuma kudi naira 10,000 daga ofishina.

“Muna godiya wa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, da kuma gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammed,” in ji Aisha Bala.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories