Wani ya faɗawa kotu cewa yunwa ce ta saka shi satar doya guda biyu

Wani mutum mara aikinyi mai suna Cletus Gandu ɗan shekara 40 a ranar Laraba ya amsa laifin satar doya guda biyu saboda yana jin yunwa.

Hukumar tsaro ta Civil Defence ce ta gurfanar da shi a gaban kotu inda ake tuhumarsa da shiga gona bada izini ba da kuma yin sata.

Gandu ya faɗawa kotun majistire dake Kafanchan a jihar Kaduna cewa ” yunwa ce ta saka ni satar doya har sau biyu ina roƙon ayimin sassauci.”

Alƙalin kotun mai shari’a, Michael Bawa ya saka ranar 6 ga watan Agusta domin yanke hukunci bayan da wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa.

Bawa ya bada umarnin a tura shi gidan yari a ajiye.

Tunda farko Marcus Audu jami’i mai gabatar da ƙara na hukumar ta Civil Defence ya faɗawa kotun cewa mai ƙorafi, Alice Daniel ita ta kai ƙorafi  a ofishin hukumar dake Kafanchan ranar 15 ga watan Yuli

Audu ya yi zargin cewa wanda ake ƙara ya saci doya daga gonar mai ƙara dake Zonkwa har sau biyu.

Ya ce laifin ya saɓa da da tanade-tanaden sashe na 327 dana 270 na kundin dokar penal code ta jihar Kaduna.

More from this stream

Recomended