Iran ta ayyana hutun makokin kwana 3 bayan Isra’ila ta kashe shugaban Hamas

Iran ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku bayan mutuwar shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a wani harin da aka dorawa Isra’ila.

A ranar Laraba, Hamas ta sanar da cewa za a yi jana’izar Haniyeh a birnin Doha a ranar Juma’a.

A ranar Alhamis ne za a gudanar da jana’izar Haniyeh a birnin Tehran. 

Nan gaba a wannan rana za a kai gawarsa Doha.

A birnin Doha, za a gudanar da addu’o’i a masallacin Imam Muhammad bin Abdul Wahhab bayan sallar Juma’a, tare da binne shi a makabartar Lusail da ke arewacin birnin.

Bikin na Doha zai samu halartar shahararru da sauran masu halarta, ciki har da shugabannin Larabawa da na Musulunci.

More from this stream

Recomended