An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa da Azzara a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Sojojin sun farma sansanonin ƴan fashin  daji dake dazukan Kurutu da kuma Hayin Dam da suka yi iyaka da Kagarko da kuma Kachia a ranar Juma’a inda wasu da yawa daga cikin ƴan fashin dajin suka tsere da raunin harbin bindiga.

Wani ɗan bijilante daga Kurutu da ya  bayyana kansa da suna, Abdullahi ya ce a ranar Litinin ne wasu manoma suka gano gawarwakin takwas a wajejen Hayin Dam.

Ya ce bayan samun labarin ne ƴan bijilante daga Hayin Dam da Kurutu suka haɗu suka je dajin domin ganin gawarwakin.

” A ranar Litinin da misalin ƙarfe 11 na safe wasu manoma sun tafi gona suka ga wasu gawarwaki sun yi kaca-kaca da harbin bindiga da ake zargi na ƴan fashin daji ne da suka tsere da raunukan harbin bindiga bayan da sojoji suka kai farmaki a sansanoninsu dake Hayin Dam da Kurutu a ranar Juma’a” ya ce.

Kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba game da batun gani gawarwakin.

More from this stream

Recomended