Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma’aikata 6 ya gamu da matsala a filin jirgin saman Yola bayan da tayoyinsa suka yi bindiga a lokacin da yake ƙoƙarin tashi daga filin jirgin.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar binciken hatsura ta ƙasa, Bimbo Oladeji  ya ce jirgin ya samu matsalar dai-dai lokacin da aka sahale masa ya tashi daga filin jirgin ya zuwa Abuja.

A dai-dai lokacin da jirgin yake shirin tashi ne aka ji wata ƙarar fashewar wani abu ashe tayoyinsa ne na gaba suka yi bindiga a yayin da sauran biyun ma suka fashe a lokacin da ake ƙoƙarin mayar da jirgin inda ake ajiye jirage.

Daraktan ya ba a samu asarar rai ba ko kuma rauni sanadiyar faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended