Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku.

Mohammed Idris, ministan yada labarai ne ya sanar da hakan a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya yi wata ganawa da shugabannin na ƙwadago a Abuja.

More from this stream

Recomended