Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin lalata da wata yarinya da wani jami’inta ya yi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kama jami’in da ake zargi da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Ogudu da ke yankin Ojota a jihar.
Kakakin ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adegoke Fayoade, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin.
“Rundunar tana tabbatar wa jama’a cewa, kwata-kwata babu wani yunkuri na yin rufa-rufa domin irin wadannan munanan ayyuka sun saba wa ka’idar aiki da kuma da’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya.
“Don haka, CP Fayoade ya sake tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a yi mu’amala da jami’in kamar yadda dokar ‘yan sanda ta tanada da kuma doka idan aka same shi da laifi,” in ji shi.
An zargi jami’in da lalata yarinyar mai shekaru 17 a cikin ofishinsa bayan ya yi alkawarin taimaka wa yarinyar dawo mara da wayarta da ta ɓata.