Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan rasuwar mamacin.

Sai dai majalisar ta fitar da wata sanarwa kan mutuwar tare da yin alƙawarin yin ƙarin bayani anan gaba.

“Sannunku abokan aiki majalisa na alhinim sanar da mutuwar ɗan majalisa mai ci, Hon Akinremi Jagaba. Zamu cigaba da baku ƙarin bayanai kan halin da ake ciki,” a cewar gajeren sakon da majalisar ta fitar.

 

More from this stream

Recomended