A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya tabbatar masa da cewa Najeriya na aiki tukuru domin kawar da ayyukan ta’addanci, da aikata laifuka ta yanar gizo, da sauran miyagun laifuka.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da daraktan hukumar ta FBI a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya yi kira da a hada kai tsakanin Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka domin kawar da miyagun laifuka a yankin.