Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 4 a jihar Borno

Dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai dake yaƙi da ƴan ta’addar Boko Haram a yankin arewa maso gabas sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda hudu a jihar Borno.

Sojojin sun samu nasarar kashe ƴan ta’addan tare da taimakon ƴan sakai da ake kira Civilian JTF a wani farmakin kwanton ɓauna a Pulka dake ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno a ranar 30 ga watan Mayu.

Musayar wuta ce ta barke bayan da aka yi tawo mu gama tsakanin sojojin da ƴan ta’addan har ta kai ga sojojin sun kashe huɗu daga ciki.

Kamar yadda wasu majiyoyin tsaro suka bayyana sauran ƴan ta’addar sun tsere da ƙafafunsu.

More from this stream

Recomended