Majalisar dattawa ta janye dakatarwar da tayiwa Abdul Ningi sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya.
Majalisar ta dawo da Ningi ne biyo bayan kudirin da sanata Abba Moro shugaban marasa rinjaye, Osita Ngwu sanata mai wakiltar mazaɓar yammacin Enugu da kuma sanata Olalere Oyewumi mai wakiltar mazaɓar kudancin Osun suka gabatar a gaban majalisar.
A cikin watan Maris ne aka dakatar da Ningi bayan da ya yi zargin cewa an yi cushe a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.
Da yake gabatar da kudirin Moro ya ce Ningi ya riga ya shafe watanni biyu baya cikin majalisar kuma akwai buƙatar ya dawo ya cigaba da aikinsa na ɗan majalisar dattawa.
Moro ya ce ya ɗauki alhakin laifin da Ningi ya yi kuma ya na bayar da haƙuri a madadinsa.
Majalisar ta amince da kudirin bayan da aka kaɗa kuri’a ta amfani da murya inda waɗanda suka amince da kuɗirin suka yi rinjaye.