Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a rana ta 11 ta jigilar.

Rahotanni sun ruwaito cewa an yi jigilar maniyyatan da aka ambata a cikin jirage 45.

Sai dai jihohi 23 a Najeriya ba su fara jigilar maniyyata aikin hajjin 2024 ba, inji rahotanni.

More from this stream

Recomended