Shekaru hudu bayan sauke Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano, Gwamna Abba Yusuf, na jihar Kano ya mayar da shi kan karagar mulki.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a dakin taro na Art Chamber na gidan gwamnatin jihar Kano, da misalin karfe 5:16 na yammacin ranar Alhamis, bayan ya sanya hannu a kan kudirin dokar majalisar masarautun jihar Kano (Repeal) na shekarar 2024.