Edward Buba daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaron Najeriya ya ce sojoji huɗu ƴan ta’adda suka kashe ranar Lahadi a wani harin kwanton ɓauna da aka kai musu.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Buba ya ce sojojin sun fuskanci hare-haren kwanton ɓauna har sau biyu daga ƴan fashin daji a ƙauyen Kuran Mota da kuma a kan hanyar Alikere zuwa Yarmalimai dake jihar ta Zamfara.
Ɓuba ya ƙara da cewa sojoji uku sun jikkata a harin.
Ya ce sojojin sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ƴan ta’addar biyo bayan da tallafin dakarun sojan sama da suka samu a lokacin fafatawar.
” A ranar 12 ga watan Mayu dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun fuskanci harin kwanton ɓauna sau biyu daban-daban ɗaya a ƙauyen Kuran Mota da kuma akan titin Alikere-Yarmalimai a jihar Zamfara,” a cewar sanarwar.