Dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai sun samu nasarar kashe, Tahir Baga wani jigo kuma kwamanda a ƙungiyar Boko Haram a cigaba da farmakin da suke kaiwa maɓoya yan ta’addar dake Dajin Sambisa.
An kashe Tahir ne a ranar 13 ga watan Mayu na shekarar 2024 a wani gagarumin farmaki da aka yiwa laƙabi da Operation Desert Sanity III domin kakkabe ƴan ta’addar daga Shababul Umma, Garin Panel Beater da Lagara Anguwan Gwaigwai dake tsakiyar dajin na Sambisa.
Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai a kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa a lokacin farmaki dakarun sojan sun yi arangama da ƴan ta’addar inda suka yi musu ɓarin wuta har ta kai ga sun kashe Baga da kuma wasu mabiyansa a yayin da wasunsu da dama suka tsere da raunin harbin bindiga.
Tahir Baga ya kasance makusanci ga tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau kuma yana ɗaya daga cikin mutanen farko da suka kafa kungiyar ta Boko Haram a birnin Maiduguri kafin su koma Dajin Sambisa tare da su Mamman Nur, Khalid Albarnawi, Abubakar Shekau, Kaka Ali, Mustapha Chadi, Abu Maryam da Abu Krimima.