Sojojin Sun Gano Wurin Ƙera Bindiga A Jihar Filato

Sojojin rundunar samar da tsaro a jihar Filato ta Operation Safe Haven sun bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar ƙera makamai dake ƙauyen Pakachi a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Jami’in ƴada labarai na rundunar, James Oya ya ce sojojin sun gano makamai da dama da kuma harsasai tare da kama mutum guda a farmakin da suka kai masana’antar.

Oya ya ce an samu nasarar gano masana’antar ne sakamakon cigaba da jajircewa da rundunar take na raba jihar da duk wasu ɓata gari dake tayar da zaune tsaye.

Ya ce an gano wurin ne a wani saman tsauni dake kauyen na Pakachi.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin shi ne mai masana’antar ya cika wandonsa da iska amma na cigaba kokarin ganin an kamo shi domin ya fuskanci hukunci.

Bindigogin da aka gano a wurin sun haɗa da AK-47 guda biyar da kuma ƙaramar bindiga ƙirar Pistol guda 11.

More from this stream

Recomended