Hauhawar farashin kayan abinci ya zama bala’i ga ƴan Najeriya

Daga Dr. Marzuq Ungogo

A shekarar 2014, bayan na fara hidimar ƙasa an fara ban alawus ɗin likita, sai na je gida daga Gombe. Na yi wa ƙannena da iyaye ‘alheri’.

Ai kuwa mahaifina sai ya ƙi karbar kuɗin da na ba shi dubu goma ya ce sun yi yawa, kuma saboda me zan ɗorawa kaina ɗawainiya ko murmurewa ban yi ba. Mafaifiyata ta dage sai ya karɓa tun da ai ita ma ta amshi na ta.

Da a ka matsa, sai Baba ya karɓi kuɗi, ya ce to zai sayi buhun shinkafa (8,000) da katan ɗin taliya (2,000): duk wanda yaci a gidan sai na samu ƙarin lada.

Bayan ya yi haka, sai na ji daɗi sosai, sannan na yanke shawarar duk wata zan bada dubu goman a ci gaba da siya.

Har zuwa 2015 da na gama service farashin nan bai chanja da yawa ba, dubu goma za ta saya ma ka buhun shinkafa da katan ɗin taliya.

Sai dai kash, tun zuwan Mai Gaskiya lamari ya jagule! Jiya na ke ji wai buhun shinkafa ya kai 70,000. Hasbunallahu wa ni’imal wakeel! Ni kaɗai kawai sai tunane-tunane nake! Ko ya ya ma’aikatan albashi su ke yi? Oho! ‘Yan kasuwa dai da sun ji dugu-dugu sai su ƙara farashi tun daga kan mai yalo har mai kamfani. Amman albashi ya ƙi ya ƙaru dai-dai da ƙimar hauhawar farashi.

Duk duniya farashi da man dole ya na ƙaruwa duk shekara. Amman wannan lamarin na Najeriya ya wuce hankali! A cikin ƙasa da shekara goma, farashin abinci na neman ninkawa sau goma! Haba!

More from this stream

Recomended