Ƴan ta’adda sun sace sama da mutum 100 a Zamfara saboda sun kasa biyan harajin da suka ɗaura musu

Wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da mutane sama da 100 a garuruwan Mutumji, Sabongari Mahuta, Kwanar Dutsi da Unguwar Kawo da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara saboda rashin biyansu kudaden harajin da aka dora wa ƴan ƙauyukan.

An tattaro cewa ‘yan bindigar na addabar al’umma saboda ba za su iya biyan harajin da aka dora musu ba.

Wani mazaunin garin Mutumji, Alhaji Muhammad Usman ya ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 8 na dare inda suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin gudu domin tsira.

A cewar wani dan kauyen, shugaban ‘yan fashin da ke yankin, Damina, a baya ya sanya wa al’ummar yankin Naira miliyan 110 a matsayin haraji, inda ya ba su wa’adin mako biyu su bi ko kuma su fuskanci sakamakon da zai biyo baya.

“An dorawa al’ummarmu harajin N50m, yayin da aka dora N30m a Kwanar Dutsi; N20m akan Sabongari Mahuta, da N10m akan Unguwar Kawo”, in ji shi.

Wata majiya daga yankin ta ce al’ummar yankin sun fara bayar da wadannan kudade ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa jama’ar da yammacin ranar Juma’a.

More from this stream

Recomended