Gwamnatin Buhari ba ta ɗauki tsaro da muhimmanci ba—Bello Matawalle

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba ta dauki batun rashin tsaro da muhimmanci ba.

Matawalle wanda ya gurfana gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin tsaro tare da ministan tsaro, Abubakar Badaru, ya bayyana cewa ma’aikatar tsaro ta dauki sabbin jirage masu saukar ungulu don bunkasa yaki da rashin tsaro a kasar nan.

Hakan na zuwa ne kamar yadda Ministan Tsaro ya shaida wa kwamitin cewa akwai hadin kai a tsakanin Hafsoshin Tsaro na yanzu.

Mattawlle, yayin da yake magana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan tsaro, ya ce batun rashin tsaro na bukatar kulawar hadin gwiwa daga jihohi, kananan hukumomi da na tarayya.

Ya ce, “A matsayina na tsohon Gwamnan Zamfara na san abin da na shiga a kan matsalar rashin tsaro, musamman ‘yan fashi da makami, wanda wani sabon salo ne a garemu a yankin Arewa maso Yamma.

“Batun Boko Haram ba sabon abu ba ne a yankin Arewa-maso-Gabas, amma saboda abin da ya faru a gwamnatin da ta shude, ba a magance matsalar da gaske ba.

More from this stream

Recomended