Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan malaman jami’a ƴan ƙungiyar ASUU albashin wata huɗu cikin wata takwas ɗin da ba a biya su ba a lokacin da suka yi wani dogon yajin aiki.
Idan ba a manta ba, zamanin da Muhammadu Buhari yake shugaban ƙasa ƴan ƙungiyar sun yi dogon yajin aikin da ya fitar da ɗalibai daga hayyacinsu.
Wannan ya sa Shugaba Buhari a lokacin daukar matakin ƙin biyan duk wani ma’aikaci albashi muddin bai yi aiki ba.