Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun ranar samun yancin kan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar da Najeriya ta samu yan cin kai.

A ranar Lahadi ne Najeriya ke cikas shekaru 63 da samun yan cin kai daga turawan mulkin Birtaniya.

Ministan cikin gida Olabunmi Tunji-Ojo shi ne ya ayyana haka a madadin gwamnatin tarayya a Abuja.

Ya taya yan Najeriya dake gida da kasashen waje murnar bikin.

More from this stream

Recomended