Mayakan Boko Haram sun kashe manoma 10 tare da yin garkuwa da wasu da dama a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno.
Baya ga wannan harin da aka kai da yammacin ranar Asabar a filayen dake tsakanin kauyukan Bulakunkumma da Maiwa na gundumar Baram Karowa ta karamar hukumar, ‘yan ta’addan sun kuma samu N4m daga hannun wani dan kasuwa a unguwar Zannari a matsayin kudin fansa.
Wata majiya mai tushe, Ya Kalu Bukar, wacce ta tabbatar da harin, ta bayyana adadin wadanda aka sacen a matsayin hudu, amma wata majiya mai suna Goni Mohammed ta ce an sace mutane har tara.
“Sun zo zagayawa cikin gonaki don neman abinci da tsabar kudi,” a cewar Bukar.
“Lokacin da manoman suka ce ba za su iya biyan kudaden da suka nema ba, sun kashe 10 daga cikinsu, dukkansu maza, suka tafi da hudu.”