Gwamnatin jihar Borno ta ce an kammala shirye-shiryen bayar da tallafin karatu na musamman ga dalibai marasa galihu da ke karatun aikin jinya da ungozoma.
Babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Mallam Bala Isa ne ya bayyana haka a Maiduguri ranar Juma’a.
“Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum na bayar da tallafin karatu na musamman ga ‘yan asalin jihar Borno masu sha’awar karatun aikin jinya da ungozoma.
“Masu neman dole ne su sami maki a Turanci, Maths, Biology, Chemistry da Physics a jarabawar gama sakandare ta WAEC, NECO ko NABTEB.”
Isa ya ce duk masu sha’awa su mika takardar shaidarsu ga hukumar bayar da tallafin karatu kafin ranar 2 ga watan Agusta.
Idan dai ba a manta ba Zulum ya yi jawabin kaddamar da wa’adi na 2, inda ya bayyana shirin gina karin makarantun koyon aikin jinya da ungozoma guda biyu a jihar domin samar da karin ma’aikata a bangaren lafiya.