An sake sace wani fitaccen basaraken gargajiya da wasu yan bindiga suka yi a jihar Filato.
Mai martaba, Sunday Dajep shi ne hakimin gundumar Chip da kabilar Mhiship suke zaune a ciki a karamar hukumar Pankshin ta Jihar.
Majiyoyi sun bayyana cewa an yi awon gaba da basaraken ne da misalin 11 na daren ranar Laraba bayan da yan bindigar suka kutsa kai fadar sa dake Chip akan hanyar Shendam zuwa Mangu.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Filato,DSP Alfred Alabo ya ce rundunar ta samu labarin faruwar lamarin.
Inda ya ce tuni suka bi sawun yan bindigar tun bayan da suka sai samu kiran kai ɗaukin gaggawa.